Yadda Zaka Samu Aikin Police Cikin Sauki

 




Assalamu Alaikum yan uwa da Abokai yau dai mun zo muku da sabon darasi wanda ba shi muka saba kawo muku ba.


Ganin yadda kowa ke tambaya ne yasa muka yi nazarin kawo muku amsar tambayar anan.


Mafi akasarin mutane suna tambayar yadda ake bude Police ba su san ya ake yi ba kuma suna son su sani.


To shi dai aikin Police aiki ne wanda kusan kowanne shekara su kan dauki mutane da yawa, amma abin da ke ciwa wasu tuwo a kwarya shi ne yadda suke fafutukar samun wannan aikin ba su samu ba. Wasu ma sai sun cire rai da samun aikin, wasu kuma gani su ke kamar galihu ne. To duk ba wannan ba ne.


Ga Dalilan Dake Sa Mutun Ya Nemi Aikin Police Kuma Ya Rasa.

Yar Kwangila Page 31 to 35 By Mubarak A Kamba.


Danna Nan Domin Ci-gaba Da Karantawa 

1. Na farko da zamu iya cewa rashin addu'a domin komai kake nema ana son ka fara nemansa a wurin ubangijinka.

2. Na biyu kuma rashin cika ƙa'idoji da dokokin da masu daukar suka gindaya muku. 

Ga Dokoki Da Ƙa'idojin

1. Na farko ana son ya kasance kai ɗan Nigeria ne, kuma takardunka duka a Nigeria aka same su.


2. Na biyu kuma, Ana son kada shekarunka su yi kasa da 18 kuma kada su haura 25, kuma lallai shekarunka su kasance daidai a cikin kowace takardarka.

3. Na uku shi ne ya kasance kana da credit 5 idan son samu ne a takarda guda WAEC ko NECO. Idan ba a samu nasarar hakan ba to kada ya wuce WAEC da NECO din domin mafi aka sari suna amfani da takarda har uku ne kamar Nabteb.

Idan ka tabbatar ka cike wadannan dokokin to insha Allahu baka da matsalar wannan aikin da nufin Ubangiji zaka samu.

Ga Link Nan A Kasa Sai Kayi Kokari Ka Cika

Da farko dai ka fara shiga wannan link din

http://www.recruitment.psc.gov.ng/


Zaka ga wurin da aka rubuta Apply sai ka taba daga nan zaka ga wurin da aka rubuta Sign up anan kuma sai ka wurin da aka rubuta create account bayan ka yi create sai ka dawo ta gmail ɗin ka kayi confirm  da kuma login daga nan ne zaka cike duk wani abin da suke bukata.


Allah ya bada nasara.

Post a Comment

Previous Post Next Post