Yadda Ake Amfani Da Gurjiya Domin Gyara Jikin Amarya

 

Amfanin Gurjiya A Wurin Gyaran Jikin Amarya

Sanin kowa ne ita Gurjiya abinci ce mai matukar dadin gaske amma sai dai ba kowa ne ya san amfanin da ke tare da ita ba. A cikin darasin yau zamu sanar daku amfanin Gurjiya.

Gurjiya na daya daga cikin abinci masu matukar amfani a jikin dan adam. Gurjiya na da protein sosai kamar yadda masana ke kiran duk wani abinci mai protein da suna (Thermogenic) Gurjiya a cikin dan adam ta yi daban da sauran nau'ukan abinci domin kuwa tana da nauyi sosai a cikin cikin mutun. Mafi yawancin abinci suna saurin narkewa a cikin cikin mutun, amma banda Gurjiya takan dauki lokaci mai tsawo kafin narkewarta wannan ne ya sa masana su ka yi dogon bincike akan inda su ka gano wasu muhimman abubuwan da zan lissafo muku.


Masana ilmin ginannen abinci sun yi gano mutumin da ya kasance mai cin Gurjiya sosai za a same shi mutun mai matukar kuzari. 

Hanyoyi Mafi Inganci Da Ake Samun Kudi A Kafafen Sadarwa Internet 

Ga kadan daga cikin abubuwan da masana suka gano a game da Gurjiya.


Masana ginannen abinci sun yi bincike mai zurfi sun gano Gurjiya na maganin ciwon sukari a cikin jikin dan adam. Masana ginannen abinci suka sanar cewa mutumin da yake yawan cin Gurjiya to ba zai kamu da ciwon sukari ba sai dai kaddarowar Allah.

Gurjiya na da amfani sosai a wurin magance ciwon koda. Idan mutun ya kasance mai ciwon koda to ana so ya mayar da Gurjiya abincinsa a koda yaushe hakan zai taimaka masa domin dawo da ingancin lafiyar jikinsa.

Gurjiya na taimakawa sosai wurin taimakawa zuciyar dan Adam ta yadda zata iya sarrafa jini yadda Yakamata.

Idan ya kasance saura kwanaki ƙalilan akai amarya a dakin mijinta ana so ta yawaita cin Gurjiya, hakan zai taimaka mata wanda za ta yi kyau sosai gabanta zai kyau domin tana dauke warin gaban mace.

Har ila yau Gurjiya na magani wurin yakar cutar kansa kamar yadda sauran suke idan ka yawaita cin Gurjiya ba zaka kamu da cutar kansa ba sai dai ƙaddarar Allah. 


Nigerian Yahooboys Arrested By Police Officers

Gurjiya tamkar magani ce ba wai abinci kaɗai ba. Tana maganin gudawa sosai,idan mutun yana gudawa sai kuma ya mayar da Gurjiya abincinsa to zai daina gudawa.

Idan budurwa ta yawaita cin Gurjiya dukiyar fulaninta za su kasance a tsaye a kowane lokaci ba za su yi saurin faduwa ba ko da kuwa ta yi aure.

A matsayinki na amarya kada ki ce kanki kadai zaki na gyarawa har angon naki ki zan gyara shi domin idan ma ya gyaru to kanki gyaran zai kare. Gurjiya na karawa maza kuzari a yayin haduwa da iyali. Kamar yadda take kara yawan ruwan abin maza.

Kada ku dauki duk wani nau'in Abinci mai kara lafiyar dan adam da zummar ci don kawar da yunwa, ku ci domin samun warakar dalilin da yasa kuka ci. Ango da amarya su yawaita cin Gurjiya ko da na tsawon wata guda ne kafin auren su, hakan zai yi matuƙar amfane su.



Sakon Jaruma Nafisa Abdullahi Zuwa Ga Masoyanta 

Ku kasance da wannan shafin ArewacinNaija News za mu cigaba da kawo muku darussa masu matukar amfani

Post a Comment

Previous Post Next Post