Fitacciyar Jarumar Kannywood Nafisa Abdullahi Tace Burinta Ya Fara Cika




 •Fitacciyar Jarumar Kannywood Nafisa Abdullahi Wacce Aka Sani Da Suna Sumayya A Cikin Shiri Mai Dogon Zango Labarina 

•Tace Burin Ta Ya Fara Cika, Domin Kuwa Ta Fara Samun Cikar Mafarkin Da Ta Dade Tanayi 

•A Koda Yaushe Burina Shi Ne In Gina Katafaren Kamfani Wanda Zai Amfanar Da Jama'a Musamman Yan Matan Wannan Zamanin 

Jarumar ta wallafa wannan batun ne a shafin na Instagram in da take nuna farin cikin gina wani Katafaren Kamfani na jikkuna wanda tun can asalin baya take da burin ginawa. A cikin shafin nata na Instagram anga inda jarumar ta saki sabon video mai dauke da hotunan jikkuna. 

Jarumar ta ce, wannan shi ne Burina da na dade ina neman cikarsa amma yau Allah ya cika min wannan babban burin nawa.

Fitacciyar Jarumar ta ce idan Allah ya nufa za'a kaddamar da wannan kamfanin ne a 14 ga watan Augusta. A jikin jakar akwai wani rubutu NAAF wanda ke nufin sunan kamfanin nata kenan. 


Nau'in Cancer Biyar Da Kuma Yadda Ake Maganceta 



Masoyanta da yawa sun tayata farin cikin samun Cikar wannan burin nata. 

Wani yanayi nake jin kai na idan na kalli yadda mafarkaina ke ta cika. Ina matukar son ganin na dauko jika mai dauke da sunana ina yawatawa a ko ina fadin duniya. Tun a waccen shekarar wannan burin nawa ya cika, to amma sai wannan shekarar ne na ji yafi da cewa na kaddamar da kamfanin kuma in sanar da masoyana. 

•Bayyanar Wani Bidiyon Wata Babbar Mota Da Jarumar Ta Siya A Cikin Kwanakinnan.

Wannan lamarin ya janyo ka ce na ce a fadin Nigeria da ma duniya baki daya. Wasu mutanen sun yi ta taya ta farin cikin Cikar wannan mafarkin nata na lonce babbar mota mai kudi kimanin Naira miliyan talatin.

Wasu kuma sun yi ta fade-faden su kan wannan batun. Jarumar ta nuna farin cikinta sosai yadda masoyanta ke taya ta dukan wani farin ciki idan ya samu.

Post a Comment

Previous Post Next Post