Ya Matsayin Zuma Da Madara A Jikinmu. Duk Wata Matar Aure Yakamata Tasan Wannan.
Ko da gaske ne zuma da madara na karawa mata ni'ima? Wannan shi ne abinda zamu tattauna a safiyar yau.
BBC Hausa sun yi fira da ma'aikaciyar Lafiya akan matsayin Zuma Da Madara a wannan zukatan namu.
Ma'aikaciyar ta ce ki "nemi zuma da madara ki jarraba amfani dasu zaki ban labari akan ni'imarki. Akodayaushe mata na magana ne akan yadda zasu karowa mai gida ni'ima, amma mafi yawanci basu san yadda tasirin zuma yake a jikinsu ba.
Hanyoyi Mafi Inganci Da Ake Samun Kudi A Kafafen Sadarwa Internet
Wasu na tambaya cewa shin da gaske na karawa mata ni'ima? A cewar ma'aikaciyar, "ba mata kadai ba har namiji wanda yake aiki da zuma zai yi bam-bam da wanda baya aiki da su.
ZUMA DA MADARA.
Madara da zuma hadi ne wanda ke matukar karawa jikinmu lafiya da kuma jin dadin jima'i a yayin saduwa da iyalanmu.
Karfin kashi da kuma samun bacci cikin nutsuwa har ma da inganta lafiyar zuciya hadin madara da zuma yana taimakawa sosai.
Ma'aikaciyar da BBC Hausa suka tattauna da ita kan matsayin Zuma Da Madara ta shaida musu cewa tabbas ba abin da ya fi su karin lafiya da jindadin jima'i, amma ayi amfani da madara shanu tafi kowace madara tattara sinadaran da ake bukata.
ABUBUWAN DA SUKE KARAWA A JIKINMU.
Madara da zuma na kara karfin kuzari da kuma saukar da ni'ima da kuma kara karfin maniyi ga maza. Idan ana neman ciki da wuri ayi amfani da zuma da madara suna taimakawa sosai. Zuma kawai ma na dauke da sinadarin calcium wanda ke kara karfin kashi. Ita kuma madara protein ce a matakin farko wacce take kara karfin kashi. Zuma na kara daidai kwayoyin halitta a turance ake cewa harmonal imbalance wanda shi ke sa a samu gamsuwa a wurin jima'i.
Suna daidaita fitar wasu halitta a jikin matanmu, kamar fitar gemu, girman tumbi da kuma rashin haila kan lokaci.
GARGADI AKAN SHAN ZUMA DA MADARA.
A lokacin da BBC Hausa ke fira da kwararriyar ma'aikaciyar lafiya wato Maijidda ta shaidawa BBC Hausa cewa kuskure ne babba mata masu dura zuma a farjinsu da sunan karin ni'ima da gamsuwa a wurin jima'i yin hakan na haifar da cututtuka kamar kaikayin gaba wanda warkewarsa ke da matukar wahala.
Post a Comment