Wata Muhimmiyar Sanarwa Zuwa Ga Masoya Kallon Shirin Labarina Daga Darakta Mallam Aminu Saira


 Kamar yadda masu kallon shirin nan mai dogon zango wanda ya samu ingantaccen aiki daga kwararrun ma'aikatan Kannywood wato Labarina, su ka sani an dauki tsawon lokaci ba a haska Film din ba a tashar arewa24.

A cikin yan kwanakin nan ne shugaban kamfanin da ke shirya Film din wato Mallam Aminu Saira ya yi wata sanarwa a cikin wani video da ya sake a shafinsa na Instagram da ma YouTube. 


Wata Hanyar Da Zaki Bi Ki Kasance Cikakkiyar Mai Ni'ima Ba Mallam Ba Boka

Director ya ce, da farko dai yana bawa masu kallon shirin hakuri a dalilin tsaikon kawo muku shi da akayi, wanda hakan ya samu asali ne a bisa wani dalili. 

Ya ce, da sun yi niyyar kawo shi a farkon wannan watan na 7 July. To amma a yanzu a bisa wannan dalilin yasa suka kai shi karshen wannan watan.

Director ya ce, mutane da yawa suna yawan tambayarsa ko meyasa ba a dora musu season 1 a YouTube channel ba? Sai shi kuma ya ba su amsa da cewa, dalilin da yasa ba su dora shi a channel ɗin su ba shi ne wani kamfani ne suke da contract a tsakaninsu, to amma wannan contract din na su ya kare.

Ya ce, haka kuma wasu ke tambayarsa shin ko da wacce Jaruma za su maye gurbin Jaruma Nafisa Abdullahi wacce aka fi sani da Sumayya a cikin shirin? Ya ba su amsa kamar haka. Har yau ba wanda ya san wacce Jaruma ce, ba mamaki a cigaba da yin shirin da jarumar da ta faro tun farko wato Nafisa Abdullahi ko kuma mu ce Sumayya.

Bayan wannan sanarwar ya kara da cewa bayan wannan Film na Labarina akwai wani sabo da za su fara nan ba da jimawa ba insha Allah.

Post a Comment

Previous Post Next Post