Wasu Application Masu Matukar Amfani A Wayarmu Ta Hanunu

 


manhajad basu san mutane basu san su ba, wasu kuma ko da an san su ba san amfaninsu ba.


Kana amfani da babbar wayar hannu amma baka san manhaja ko daya ba wacce take karawa wayarka inganci ko kuma kariya da sauransu ba. Maganar gaskiya ba da waya kake amfani ba, sai dai mun ce gwangwani. Eh mana gwangwani tunda akwai manhaja da yawa wanda zasu amfane ka amma baka san su ba kuma ka gaza ka neme su domin cigabanka.

Ga jerin manhajojin da zaka amfana da su a wayarka ta hannu.


1. Scratch Scanner.

Amfanin scratch Scanner shi ne loda kati. A duk lokacin da kake so ka loda kati ko cikin taro ko kuma kana kan baka da lokacin da zaka loda kati da hannunka abinda kawai zaka yi ka yi kokarin download na Scratch Scanner a cikin   ka bude shi zai kawo maka Camera sai ka dauki hoton katin nan take zai ciro numbobin sai kawai ka karasa sauran code din.



2. Ludo Master.

 Wannan wasa ce wacce ake yi da wani karamin faranti da dice a ciki shi ne aka yo manhajarsa. Abinda yasa muka kawo mu ku shi a cikin wannan posting shi ne Ludo Master wasa ce mai matukar dadi musamman ga ma'aurata. Oga zai iya download din ta ya zo gida su buga tare da uwar gida ko amarya ko ma ka hade su dukan su biyu ku buga idan biyu gareka kai kai koma hudu gareka zaku iya yi tare cikin farin ciki.


3. VPN.

 Har yau wasu ba su san amfanin VPN ba duk da yake suna gani ana tallarsa a wuraren download da dama. Amfanin VPN shi ne karawa waya karfin network, wani VPN din ma sai ya na baka kyautar data.


4. KineMaster. 


Amfanin KineMaster shine editing na video komai tsawonsa ko ma mu ce yawansa za a iya gyara shi yadda ake so da KineMaster. Masu aikin YouTube ma da KineMaster suke amfani wurin gyaran video.


5. PixelLab.

Wannan shi ne babban manhajar wayar hannu wanda ake amfani da shi wurin gyaran duk wani hoto da aka yi.


6. Remove.bg


Shi ma wannan manhaja ne wanda ake amfani da shi idan za a cire background na hoton.




Post a Comment

Previous Post Next Post