Kungiyar ECOWAS Ta Gargadi Shugaban Kasar Nigeria Da Kada Ya Sake Rufe Shafin Twitter.
ECOWAS ta gargadi kasar Nigeria a karkashin shugabancin Muhammad Buhari da kada ta sake yin kuskuren da ta yi a baya na rufe shafin Twitter.
Shugaba Malcolnm Emokiniovo Omirhobo ne dai ya shigar da karar, a cewarsa rufe shafin sada zumunta domin wani babban zalunci ne ga jama'ar da ke aiki da shafin.
Ya kuma ce yin hakan ya zama hana walwala ga jama'ar da ke aiki da shafin.
Kotun da Malcolnm ya kai kara ta gargadi kasar Nigeria da kada ta sake maimaita irin wannan kuskuren da ta yi a can baya idan kuwa ta kuskura ta sake yi zata fuskanci hukunci.
A baya dai kamar yadda masu aiki da shafin suka sani shugaba Muhammad Buhari ya sa aka rufe shafin Twitter a dalilin goge wani rubutu da yayi akan martani ga yan Biafra. Wannan shine dalilin da yasa aka gargadi kasar Nigeria.
Post a Comment