A ranar goma ga watan Yuli ne Alh. Ibrahim Masari ya janye daga neman kujerar mataimakin shugaban kasa. Bayan dogon nazari da tunanin da Alh. Ahmed Bola Tinubu yayi ya gano Tsohon gwamnan Borno Alh. Kashim Shettima ne yafi cancanta da zama mataimakin shugaban kasa, wanda kungiyar CAN wato kungiyar Kiristocin Nigeria suka maganta akan hakan domin kuwa kamar anyi ba daidai ba ne Musulmi ya zabi musulmi a matsayin mataimakinsa a cewarsu.
A lokacin Alh. Ahmed Bola Tinubu ya kaiwa shugaban kasar Nigeria General Muhammad Buhari ziyara a matsayin barka da sallah ya sanar da manema labarai cewa ya zabi Alh. Kashim Shettima mataimakinsa ne domin kasancewarsa mai gaskiya da rikon amana wanda ba zalunci da ha'inci a rayuwarsa. Ya kuma ce yana son masu maganganu kan kabilanci na ganin musulmi ya zama mataimakin musulmi ba daidai ba ne su gane duba cancanta tafi kyau fiye duba kabilanci ko addini a siyasance.
Alh. Ahmed Bola Tinubu dan takarar siyasar shugaban kasar Nigeria a karkashin jam'iyyar APC (All Progressive Change) ya ce ya zabi Alh. Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa ne domin ya kasance mai son cigaban kasarsa Nigeria. Yana kuma fatar Allah ya basu ikon yin gaskiya idan sukayi nasara dalewa akan kujerar.
Alh. Ahmed Bola Tinubu Ya Zabi Kashim Shettima A Matsayin Mataimakinsa
Arewacin Naija News
0
Tags
Labaran Siyasa
Post a Comment